20 Mayu 2025 - 21:08
Source: ABNA24
Hamas: Kawo Yanzu Babu Wani Agaji Da Ya Shiga Yankin Zirin Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Palasdinawa ta Hamas ta sanar da cewa: Ya zuwa yanzu babu wani agaji da ya shiga yankin zirin Gaza, kuma manyan motocin da suka isa mashigar Karm Abu Salem babu wata hukumar kasa da kasa da ta karɓe su.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Kungiyar Hamas ta fitar da wata sanarwa a yau Talata tana mai cewa: tare da ci gaba da kasancewar tawagar 'yan sahayoniya a birnin Doha, duk da cewa ba ta da tabbatacin hurumin cimma matsaya, wannan wani yunkuri ne kawai na Netanyahu na yaudarar ra'ayin jama'a da cewa kayyayakin agaji sun shiga Gaza.

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta kuma yi nuni da cewa, firaministan kasar Isra'ila yana bayyana karya ne game da halartar tattaunawa, yana mai cewa: Ana tsawaita zaman tawagar Isra'ila a birnin Doha a kowace rana, amma ba ta fara wani muhimmin tattaunawa ba, kuma tun ranar Asabar din da ta gabata ba a fara wata tattaunawa ta hakika ba.

Gwagwarmayar Falasdinu ta ci gaba da cewa: Kalaman Netanyahu na kai agajin jin kai a zirin Gaza kawai don bata suna da kuma yaudarar al'ummar duniya ne; Domin kawo yanzu babu wata motar dakon kaya da ta shiga zirin Gaza.

Your Comment

You are replying to: .
captcha